Gwamnatin Kano ta ayyana ranar Talata, 16 ga watan Yuni, 2026, a matsayin ranar hutu domin bikin sabuwar shekarar Musulunci ta 1448 Hijiriyya.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar.
Sanarwar ta ce GwamnaAbba Kabir ya kuma taya al’ummar Musulmi murnar shiga sabuwar shekarar ta Musulunci, wadda ta fara da watan Muharram, wato watan farko a kalandar Hijiriyya.
Gwamnan ya yi kira ga al’ummar jihar da daukacin al’ummar Musulmi da su yi nazari kan ayyukansu na shekarar da ta gabata tare da amfani da wannan dama wajen yin addu’o’i na musamman domin samun zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban Kano da Najeriya baki ɗaya.
Ya kuma bukaci jama’a da su ci gaba da rungumar kyawawan ɗabi’u, haƙuri, tausayi da taimakon juna, waɗanda addinin Musulunci ya koyar, domin ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin al’umma..
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamnan na jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da ingantattun manufofi da shirye-shiryen da suka shafi jin daɗin jama’a da inganta rayuwarsu ta hanyar shugabanci na gaskiya, adalci da kishin talakawa.
