Cibiyar gyaran halaye da kula da masu shaye-shayen miyagun ƙwayoyi ta Kiru da ke Kano, ta ce yawan mutanen da ke buƙatar kulawarta ya zarce ƙarfin wuraren da take da su.
Shugabar cibiyar, Cheryl Amina Kwagga, ce ta bayyana hakan yayin ziyarar da tawagar Premier Radio ta kai cibiyar ranar Alhamis.
Ta ce cibiyar tana da ƙarfin ɗaukar mutum 258, tana mai cewa akwai buƙatar kafa ƙarin cibiyoyi masu irin wannan aiki, waɗanda za su iya kula da mutane fiye da dubu ɗaya.
Cheryl Amina Kwagga ta kuma bayyana cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayar da wata cibiya makamanciyar ta Kiru a Ƙaramar Hukumar Gaya, wadda aka ware domin kula da mata masu fama da matsalar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.
A nasa jawabin, Shugaban Sashen Gudanarwa na cibiyar, Attahiru Musbahudeen, ya ce tun bayan buɗe cibiyar a watan Fabrairun 2026, ta taimaka wa mutane 250 wajen kammala shirin gyaran halaye.
Ya ƙara da cewa sama da mutane 500 sun kuma amfana da ayyukan cibiyar ta hanyar zuwa neman taimako ba tare da kwana a cikinta ba.
A cewar shugabar cibiyar, a halin yanzu akwai mata 11 da maza 258 da ke karɓar kulawa a cibiyar, lamarin da ke ƙara nuna buƙatar faɗaɗa wuraren kula da masu fama da matsalar shaye-shaye.
