Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya bayyana alhinin rasuwar Sarkin Gumel, Alhaji Ahmed Muhammad Sani II, a matsayin babban rashi ga jiharJigawa, masarautar Gumel.
Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar.
Gwamnan Abba ya bayyana marigayin da cewa Sarkin da cewa basarake ne mai mutunci, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen tabbatar da zaman lafiya, hadin kai da ci gaban al’ummar masarautarsa.
Gwamnan ya kuma roki Allah da ya gafartawa marigayin kura-kuransa, ya sanya shi cikin aljannatul firdaus, tare da baiwa iyalansa da al’ummar Gumel juriyar jure babban rashin.
Haka kuma, Gwamna Yusuf ya bukaci al’ummar jihar Jigawa da su yi hakuri, tare da yin koyi da kyakkyawan tarihin hidima da shugabanci da marigayi Sarkin ya bari a baya.
