
Aminu Abdullahi Ibrahim
Ƙungiyar Population Services International (PSI) Nigeria ta bayyana nasarorin da ta samu a ƙarƙashin shirin inganta lafiyar jinin al’ada na mata da ‘yan mata, wato Menstrual Health – No Wahala (MH-NOW), a jihar Kano.
Hakan na zuwa ne bayan kammala shirin da kuma miƙa ragamar ci gaba da ayyukansa a wani taro da aka gudanar ranar Alhamis a Kano.

Shirin, wanda ya mayar da hankali wajen yaƙi da kyama da kunyar da ake dangantawa da jinin al’ada, tare da inganta lafiyar mata da ‘yan mata, ya gudana a ƙananan hukumomin Nassarawa, Ghari da Garun Malam.

Da take jawabi a wajen taron mai taken “Breaking Menstrual Stigma: Three Years of Care, Confidence and Change for Women and Girls”, jami’ar kula da shirye-shiryen PSI a Kano, Amina Sabia Musa, ta ce shirin ya samu nasarori a muhimman fannoni uku.

Ta bayyana cewa fanni na farko shi ne ƙarfafa tattalin arzikin mata, ta hanyar gano tare da tallafa wa masu sana’ar ƙera audugar mata ta cikin gida, da kuma masu rarraba kayayyakin domin tabbatar da samuwarsu cikin sauƙi da araha a cikin al’ummomi.
A cewarta, shirin ya kuma samar da tallafin jari ga masu ƙera audugar domin ƙarfafa sana’o’insu tare da rage matsalar rashin kuɗin sayen kayayyakin tsaftar jinin al’ada.
Amina ta ce fanni na biyu ya mayar da hankali kan wayar da kan jama’a game da lafiyar jinin al’ada, tsafta da ilimi, ta hanyar gudanar da kamfen a makarantu, al’ummomi da cibiyoyin kula da lafiya matakin farko.
Ta ƙara da cewa fanni na uku shi ne tallafa wa ƙirƙirar manufar ƙasa kan lafiyar jinin al’ada, wadda ta bayyana a matsayin irinta ta farko a Najeriya.
Jami’ar ta yi kira ga gwamnati, ƙungiyoyin ci gaba da sauran masu ruwa da tsaki da su ci gaba da tallafa wa shirin, tana mai cewa bai kamata a ɗauki batun lafiyar jinin al’ada a matsayin matsalar mata kaɗai ba.
A kalamanta, ta ce, “Jinin al’ada ba batun mata kaɗai ba ne, batu ne da ya shafi kowa. Ba za mu iya yin aiki mu kaɗai ba. Muna buƙatar goyon bayan maza, mazajen aure, iyaye maza da ‘yan’uwa.”
Amina ta ce ƙungiyar ta shafe shekaru biyu tana wayar da kan mata da ‘yan mata game da tsaftar jinin al’ada, tare da inganta hanyoyin samun kayayyakin tsafta masu sauƙin araha.
Ta kuma buƙaci gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su tabbatar da dorewar shirin, tana mai jaddada cewa buɗe tattaunawa kan lafiyar jinin al’ada na da muhimmanci wajen gyara kuskuren fahimta da ƙarfafa mata da ‘yan mata su nemi ingantaccen kulawar lafiya.
A nata jawabin, Mataimakiyar Darakta kuma Shugabar Sashen Wayar da Kai kan Lafiya a Ma’aikatar Lafiya da Jin Daɗin Al’umma ta kasa da ke Abuja, Madiu Ezeyoma, ta ce taron ya samar da damar tantance nasarorin shirin, sauraron shaidun waɗanda suka amfana da kuma tsara hanyoyin tabbatar da dorewar ayyukan bayan kammala lokacin aiwatar da shi.

Ta bayyana cewa shirin ya taimaka wajen inganta halartar ‘yan mata makaranta, sakamakon ƙarin wayar da kai da karɓuwar batun jinin al’ada, wanda ya taimaka wajen rage kunya da kyamar da a baya ake dangantawa da shi.
Ezeyoma ta kuma jaddada rawar da sarakunan gargajiya, ƙungiyoyin al’umma da jakadun wayar da kai suka taka wajen inganta fahimtar lafiyar jinin al’ada.
Ta ce haɗa bayar da shawarwari kan lafiyar jinin al’ada da ayyukan cibiyoyin lafiya matakin farko ya ƙara ƙarfafa shirin, tare da taimaka wa mata da ‘yan mata samun ingantattun bayanai da taimakon da suke buƙata.
Jami’ar ta yi kira ga iyaye da al’umma da su ƙarfafa ‘yan mata su ci gaba da zuwa makaranta da gudanar da harkokinsu na yau da kullum a lokacin jinin al’ada, ba tare da tsoro ko jin kunya ba.
A nasu jawabin, wasu waɗanda suka amfana da shirin sun bayyana sauye-sauyen da aka samu a cikin al’ummominsu.
Wata mata daga yankin Ghari, Samira Bello, ta ce shiga cikin shirin ya ba ta damar ilmantar da mata kan muhimmancin tattaunawa da ‘ya’yansu mata game da tsaftar jinin al’ada.
Haka kuma, wata data ci gajiyar shirin, Firdausi Bello, ta bayyana cewa PSI ta tallafa wa cibiyoyin kula da lafiya matakin farko guda biyar a Ghari, inda aka gudanar da ayyukan wayar da kai da ba da shawarwari, waɗanda suka ƙarfafa ‘yan mata su riƙa tattaunawa da iyayensu cikin ‘yanci game da jinin al’ada.
Ta ce iyaye ma sun ƙara fahimtar muhimmancin kula da lafiyar jinin al’adar ‘ya’yansu, ciki har da bibiyar lokutan da suke samun jinin al’ada.
Firdausi ta yi alƙawarin cewa waɗanda suka amfana da shirin da sauran masu ruwa da tsaki a cikin al’umma za su ci gaba da wayar da kai kan lafiyar jinin al’ada duk da kammala shirin.
Ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da suka ja hankalin mahalarta taron shi ne bayar da takardun shaidar karramawa da lambobin yabo ga fitattun jakadun shirin, bisa jajircewarsu, sadaukarwarsu da gudummawar da suka bayar wajen inganta wayar da kai kan lafiyar jinin al’ada da yaƙi da kyama a cikin al’ummominsu.
