Majalisar wakilan Najeriya ta ce tana tattara sahihan bayanai daga jihohin kasar wadanda zasu taimaka mata wajen samar da dokoki da matakan da za su rage safarar miyagun kwayoyi, shaye-shaye da illolinsu ga matasa da al’ummar Najeriya.
Shugaban Kwamitin majalisar na musamman mai Yaki da shan Miyagun Kwayoyi da Taba sigari, Farfesa Jerry Sonny Ugokwe, shi ne ya bayyana hakan lokacin da ya kawo ziyarar aiki cibiyar gyaran hali ta Kiru dake Kano.
A cewar Farfesa Jerry majalisa wakilan ta dukufa wajen lalubo hanyoyi da tattara bayanan da zasu bata damar yin dokar da zata yi daidai da matsalar domin magance ta a fadin Najeriya, kuma sun zo Kano ne domin yin duba kan irin aikin da cibiyar gyaran halin ta ƙiru ke yi.
A nata jawabin Shugabar cibiyar gyaran hali ta Kiru uwargida Cheryl Aminta Kwagga, ta ce ta gayyato kwamitin majalisar Kano ne domin hada hannu da Majalisar da yin duba kan yadda ayyukan su yake gudana domin kara basu shawarwari da dabarun da doka ta tanadar wajen gyara halayen wadanda shan miyagun kwayoyi ya illata.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa kwamitin ya kai ziyarar da girmamawa ga Mai Martaba Sarkin Kano Muhammad Sanusi II, da hukumar hana sha da fataucin miyagun Kwayoyi NDLEA reshen sai kuma ofishin Sakararan gwamnatin Kano domin neman hadin gwiwar su akan kudurin da suka sanya a gaba.
