Kwamitin Raba Kuɗaɗen Asusun Tarayya, FAAC, ya raba naira tiriliyan 2.441 ga gwamnatin tarayya, jihohi 36 da ƙananan hukumomi 774 a watan Nuwamban 2026, duk da raguwar kuɗaɗen shiga da aka samu a watan Oktoba.
Adadin ya nuna ƙarin naira biliyan 13, kwatankwacin kashi 0.54 cikin ɗari, idan aka kwatanta da naira tiriliyan 2.428 da aka raba a watan Oktoba.
Ofishin Akanta-Janar na Tarayya ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Bawa Mokwa, ya fitar ranar Laraba, 18 ga Nuwamban 2026.
An amince da rabon kuɗaɗen ne a taron FAAC da aka gudanar a Abuja, inda aka yi la’akari da kuɗaɗen shiga da aka samu a watan Oktobo
Me ya sa rabon kuɗaɗen ya ƙaru?
Duk da ƙaruwar rabon FAAC, jimillar kuɗaɗen shiga da aka samu a watan Oktoba ta ragu da naira biliyan 102, daga tiriliyan 3.913 a watan Satumba zuwa tiriliyan 3.811.
Haka kuma, kuɗaɗen shiga na yau da kullum sun ragu daga tiriliyan 3.096 zuwa
