Ƙungiyar agajin lafiya ta ƙasa da ƙasa, Médecins Sans Frontières (MSF), ta bayyana cewa sama da mutane 1,260 ne suka mutu sakamakon cutar mashako (Diphtheria) a Najeriya tun bayan ɓarkewarta a ƙarshen shekarar 2022.
A wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Manema Labarai na ƙungiyar, Abdulkareem Yakubu, ya fitar, MSF ta ce an samu sama da mutane 41,000 da ake zargin sun kamu da cutar, yayin da aka tabbatar da fiye da 24,000.
Ƙungiyar ta ce daga watan Janairu zuwa 9 ga Agustan 2026 kaɗai, an tabbatar da kamuwar mutane 10,476, yayin da 406 suka mutu.
MSF ta yi gargaɗin cewa ƙarancin maganin Diphtheria Antitoxin da rashin isasshen rigakafi na ƙara barazana ga rayukan jama’a, musamman a jihohin Kano, Katsina, Kaduna, Bauchi, Borno, Filato, Sokoto da Zamfara.
Kodinetan Kula da Lafiya na MSF a Najeriya, Dakta David Kizito, ya jaddada muhimmancin samun magani cikin gaggawa, musamman a sa’o’i 48 na farko bayan bayyanar alamomin cutar.
