A wani mataki na ƙara kaimi wajen yaƙi da sauyin yanayi da kare muhalli, Cibiyar Bunƙasa Fasahar Sadarwa da Ci Gaban Al’umma (CITAD) ta ƙaddamar da shirin dasa bishiyoyi a makarantu a Jihar Kano.
Babban Daraktan cibiyar, Injiniya Yunusa Zakari Ya’u, ne ya jagoranci ƙaddamar da shirin tare da dasa bishiyoyi a Makarantar Ilimi ta Musamman da ke Tudun Maliki a Kano.
Cibiyar ta bayyana cewa shirin zai kai ga dukkan makarantun sakandare na gwamnati a faɗin jihar, domin ƙarfafa ɗalibai su kasance masu taka rawa wajen kare muhalli da rage illolin sauyin yanayi.
CITAD ta ce manufar shirin ita ce bunƙasa al’adar dasa bishiyoyi a tsakanin ɗalibai, tare da wayar musu da kai kan muhimmancin kare muhalli domin samar da kyakkyawar makoma ga al’umma.
