Jam’iyyar Labour Party LP, ta sanar da dage zabukan fidda gwani na shugaban ƙasa, Gwamnoni, ‘yan majalisar wakilai da na jihohi zuwa ranar 30 ga watan Mayu, 2027.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar na ƙasa, Ken Asogwa ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka fitar a Abuja a yau Alhamis.
Da fari dai jam’iyyar ta tsara gudanar da zabukan fidda gwani na Gwamnoni da ‘yan majalisar jihohi ranar 27 ga watan Mayu, yayin da na shugaban ƙasa da majalisar tarayya aka shirya yi ranar 29 ga watan Mayu.
Sai dai Asogwa ya ce yanzu za’a gudanar da dukkan zabukan a rana guda, wato ranar 30 ga watan Mayu.
A cewarsa, an dauki matakin ne saboda jadawalin farko ya yi karo da wasu muhimman bukukuwa na kasa.
Jam’iyyar ta kuma bayyana cewa an dauki matakin ne domin tabbatar da hadin kai da mutunta al’amuran kasa, tare da nuna nadama kan duk wata matsala da sauyin jadawalin ka iya haifar wa masu ruwa da tsaki da sauran al’umma.
