Hukumar REMASAB ta gudanar da shirin duba lafiyar mutane 2,000 da raba musu magunguna KYAUTA da tallafin jari a ƙananan hukumomin Shanono da Bagwai, domin tallafawa al’umma da inganta lafiyarsu.
Shugaban hukumar Dr Muhammad S. Khalil, ne ya ƙaddamar da shirin, inda ya ce an shirya tsarin ne da haɗin gwiwar hukumar taimakekenjyar lafiya ta Kano domin ragewa al’umma raɗaɗin matsin tattalin arziƙi da kusantar da ayyukan jin ƙai zuwa ga waɗanda suka fi buƙatarsu.
Dr. Khalil ya ce shirin na daga cikin ƙudirin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na inganta walwalar jama’a, ƙarfafa ƙananan sana’o’i da samar da hanyoyin dogaro da kai, musamman ga masu ƙaramin ƙarfi, yana mai jaddada aniyar gwamnatin Kano na ci gaba da shirye-shiryen tallafawa al’umma.
Shi ma shugaban ƙaramar hukumar Shanono, Abubakar Barau, ya yi maraba da shirin tare da kira ga waɗanda suka amfana da tallafin da su yi amfani da shi yadda ya kamata wajen bunƙasa sana’o’insu da inganta rayuwarsu.
