Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya ce kawunan ‘yan siyasar Kano yanzu ya fi haduwa fiye da kowane lokaci a tarihin siyasar jihar.
Gwamnan ya bayyana haka ne, lokacin da Kwamitocin da uwar jam’iyyar APC ta kasa ta turo domin sanya ido kan zaben shugabannin jam’iyyar a matakin mazabu da Kananan Hukumomi ya gudana suka kai masa ziyara.
- Allah Yai mana maganin munafikan da ke son mu ɓata da Kwankwaso – Gwamna Abba
- Hotuna: Bikin Karbar Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Zuwa Jam’iyyar APC
Gwamna Abba ya ce tun bayan shigar sa da wasu manyan ‘yan siyasa, jam’iyyar APC ke ci gaba da samun hadin kai a fadin jihar, inda rarrabuwar kai ke raguwa.
Gwamnan ya kuma yabawa kwamitocin bisa nasarar gudanar da zabukan Shugabannin mazabun da kananan hukumomi cikin nasara a fadin jihar.
Tun da farko a jawabin sa, Shugaban Kwamitin Malam Lantep Dabang, ya godewa Gwamnan bisa tausayi da kyakkyawan jagoranci da ya nuna, musamman wajen rabon mukaman jam’iyya cikin adalci.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito malam Lantep na bayyana Gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin shugaba mai rikon amana da adalci.
