Gwamnatin Kano ta amince da kashe kuɗin da yawan su ya zarce naira biliyan 2 da miliyan 650, domin gyarawa da yin sauye-sauyen bututun ruwa a wurare daban-daban, da nufin tabbatar da ganin ruwan famfo na zuwa lungu da saƙon jihar, a yunƙurin ta na wadata al’umma da ruwa mai tsafta.
Kwamshinan yada labarai da harkokin cikin gida na Kano Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala zaman majalisar zartarwar jihar karo na 42 wanda ya gudana a tsakar daren Lahadi zuwa wayewar garin yau Litinin.
Kwamshinan ya ce amincewa majalisar ya biyo bayan ƙwazon da gwamnati ta nuna na yiwa matsalar ruwan da ta jima tana damun Kano kwaf ɗaya, wanda hakan ya sanya ruwan famfo ya ɓalle tare da ƙoƙarin yin ɓarna a wasu sassan Kano saboda ji awar da suka yi basa aiki wasu wuraren kuma al’umma sun haƙe su sun yi gine-gine a hanyar ruwan.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Kwamishinan na cewa gwamnatin Kano ta sha alwashin ci gaba da yin duk mai yiwuwa domin farfado da dukkan matdatsu da matattun ruwan da take da su tare da samar da wasu sababbi, ƙoƙarin mayar da matsalar ruwan famfo tarihi a ƙwaryar birni da kauyykan jihar.
