Aminu Abdullahi Ibrahim
An samu barkewar rikici yayin nada sabon dagacin Madobi bayan rasuwar tsohon dagacin Alhaji Umaru Mahmud.
Wannan na zuwa ne bayan da masu neman kujerar dagacin suka kalubalanci salon da suka ce hakimin Madobi Alhaji Saleh Musa Saleh ya bi domin zabar sabon dagaci.
Tafidan Madobi guda daga cikin masu neman kujerar Dagacin Madobi Alhaji Hussain Sarki Aliyu Rabakaya, ya ce bai gamsu da tsarin da hakimin Madobi yazo dashi ba a zaben kujerar.
Hussain Tafida wanda Dakta Usman Sarki Sulaiman ya wakilta ya ce ko kadan ba a bi tsarin da ya dace ba domin ya sabawa al’ada kuma ba zasu amince da hakan ba.
Haka zalika ya yi zargin cire sunayen wasu dage neman kujerar da sanya wasu da basa cikin tsarin.
Dangane da korafin mun tuntubi hakimin karamar hukumar Madobi Alhaji Saleh Musa Saleh, sai dai yaki cewa komai akan batun.
