Abba Atiku Abubakar, ɗan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana aniyarsa ta ganin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu nasara a jihar Adamawa a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Abba ya bayyana hakan ne ranar Juma’a a hedikwatar jam’iyyar APC da ke Abuja, yayin taron manema labarai na ƙaddamar da manufofin ƙungiyar Haske Bola Tinubu Organisation (HBTO), wadda ya kafa kuma yake jagoranta.
Ya ce goyon bayan da yake bai wa Tinubu zaɓinsa ne na kansa, wanda ya yi bisa imaninsa da manufofin siyasa, ba tare da la’akari da matsayin mahaifinsa a siyasa ba.
Abba ya ƙara da cewa kowane mutum yana da ‘yancin zaɓar jam’iyya ko ɗan takarar da yake ganin ya dace da shi, ko da kuwa ra’ayinsa ya bambanta da na iyalansa.
A yayin taron, ƙungiyar HBTO ta kuma bayyana wani shiri na samar da sufuri mai rahusa ga jama’a a Babban Birnin Tarayya, Abuja.
