Atiku Ya Yi Alƙawarin Dawo Da Martabar Sarakunan Gargajiya Idan Ya Zama Shugaban Ƙasa.
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin dawo da martaba da ƙarfafa ikon sarakunan gargajiya idan ya samu nasarar zama shugaban Najeriya a zaɓen 2027.
Atiku ya bayyana hakan ne yayin ziyarar ban girma da ya kai wa Sarkin Bauchi, Dakta Suleiman Rilwanu Adamu, a fadarsa, gabanin gangamin siyasar jam’iyyar ADC da aka shirya gudanarwa a jihar ranar Asabar.
Ya ce ƙarfafa rawar da sarakunan gargajiya ke takawa zai taimaka wajen magance wasu matsalolin da Najeriya ke fuskanta.
A nasa jawabin, Sarkin Bauchi ya nuna farin cikinsa da ziyarar, tare da kira ga ’yan siyasa su gudanar da harkokinsu cikin mutunta juna da zaman lafiya.
