Shugaban Karamar Hukumar Ghari Hashimu Garba Mai sabulu ya jagoranci raba takardun kama aikin gwamnati ga sabbin malamai 81 da malamai ‘yan BESDA 50 da kuma bayar da takardun guraben karatu ga matasan karamar hukumar.
A wajen taron, an kuma baiwa wasu mutane 11 takardun kama aikin koyarwa a Kwalejin Yusuf Maitama Sule da ke Karamar Hukumar ta Ghari, tare da sanar da gurbin karatu ga matasa 16 ‘yan asalin Karamar Hukumar Ghari a kwalejin koyon aikin jinya.
Da yake jawabi a wajen, Shugaban Karamar Hukumar, Hashimu Garba Maisabulu, ya ce rabon takardun aikin gwamnatin da na karatu, wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamna Abba Kabir Yusuf na bunƙasa harkar ilimi da samarwa al’ummar jihar makoma me kyau.
Maisabulu ya hori waɗanda suka amfana da tsarin da su yi kyakkyawan amfani da shi ta hanyar da ta da ce, da jajircewa wajen gudanar da aikinsu da karatunsu domin bayar da gudunmawa wajen ci gaban Karamar Hukumar Ghari da Kano baki daya.
