Gwamnatin Kano ta bukaci mata masu juna biyu da su rungumi zuwa asibiti tun daga farkon lokacin da suka tabbatar suna ɗauke da juna biyu, domin samun kulawar likitoci da kuma kare lafiyarsu da ta jariran da za su haifa daga kamuwa da cututtuka masu yaɗuwa, musamman cuta mai karya garkuwar jiki.
Kwamishinan lafiya na Kano, Dr Abubakar labaran Yusuf ne ya bayyana hakan yayin wani taron wayar da kai da aka shirya domin ƙarfafa gwiwar mata masu juna biyu su fara zuwa cibiyoyin lafiya da wuri domin samun kulawar da ta dace.
Dr Labaran ya ce yin rajistar kula da masu juna biyu tun da wuri na taimakawa wajen gano duk wata matsalar lafiya cikin lokaci, tare da bada maganin da ya dace, wanda hakan ke kare lafiyar uwa da jariri.
Shi ma a nasa jawabin, Shugaban Hukumar yaƙi da yaduwar cuta mai karya garkuwar jiki ta Kano Dr Usman Bashir, ya ce an shirya taron ne domin ƙara wayar da kan al’umma kan muhimmancin kare jarirai daga kamuwa da cututtukan da kan iya yaɗuwa daga uwa zuwa ɗa.
Wakilinmu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa shugabannin biyu sun kuma yi kira ga mata masu juna biyu da su rika zuwa cibiyoyin lafiya domin yin gwaje-gwaje, samun shawarwari da kuma karɓar magungunan da suka dace, domin tabbatar da haihuwar yara masu ƙoshin lafiya.
