Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da zagaye na hudu na shirin SARMAAN II, tare da zagaye na biyu na makon kula da lafiyar mata masu juna biyu, jarirai da kananan yara na shekarar 2026, domin inganta lafiyar al’umma da rage mace-macen mata da kananan yara.
An gudanar da bikin kaddamar da shirye-shiryen ne a cibiyar ayyukan gaggawa ta lafiya ta jihar Kano, inda wakiliyarmu, Halima Ayyuba Adamu, ta halarta.
Zagaye na hudu na shirin SARMAAN II zai mayar da hankali ne kan tabbatar da ingantaccen amfani da maganin Azithromycin ga kananan yara masu shekaru daga wata daya zuwa watanni 59, tare da sa ido kan matsalar juriyar kwayoyin cuta ga magungunan kashe su.
Da yake jawabi a wajen taron, kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya bayyana cewa bincike ya nuna an samu raguwar mace-macen yara a jihar sakamakon amfani da maganin.
Ya kara da cewa a wannan zagayen, ana sa ran shirin zai kai ga yara miliyan uku da dubu dari bakwai da goma sha takwas (3,700,018).
Haka kuma, za a shafe kwanaki bakwai ana gudanar da makon kula da lafiyar mata masu juna biyu, jarirai da kananan yara, inda za a gudanar da ayyuka daban-daban da suka hada da rigakafi, bayar da sinadarin Vitamin A da sauran muhimman ayyukan kula da lafiyar mata da yara.
Gwamnatin jihar Kano ta yi kira ga iyaye da su fito da ‘ya’yansu domin amfana da ayyukan da aka tanada a cibiyoyin lafiya da sauran wuraren da za a gudanar da shirin.
Haka kuma, jami’an lafiya za su rika zagayawa gida-gida domin tabbatar da cewa yara sun samu damar cin gajiyar ayyukan da aka tanada a karkashin shirin.
