Shugaban Ghana, John Dramani Mahama, ya ba da umarnin kafa tawaga ta musamman ta haɗin gwiwa domin ƙarfafa matakan tsaro a iyakokin ƙasar, musamman a tashoshin jiragen ruwa.
Matakin na zuwa ne bayan hukumomin Faransa sun kama kusan tan 3.9 na hodar iblis a tashar jiragen ruwa ta Dunkirk, wadda bincike ya nuna cewa ta fito ne daga tashar Tema da ke Ghana.
An kiyasta darajar miyagun ƙwayoyin da aka kama da kusan dalar Amurka miliyan 261, inda aka ɓoye su cikin kwantenoni kafin jami’an tsaro su gano tare da cafke su.
Binciken farko da hukumomin Ghana suka gudanar ya kai ga kama wasu mutane da ake zargi da hannu a safarar miyagun ƙwayoyin.
Daga cikin waɗanda aka kama akwai jami’an hukumar kwastam guda huɗu, waɗanda kotu ta tura gidan yari domin ci gaba da bincike, ba tare da ba su damar beli ba.
Gwamnatin Ghana ta kuma yi alƙawarin yin aiki kafada da kafada da hukumomin ƙasashen duniya domin gano tare da cafke dukkan mutanen da ake zargi da hannu a safarar miyagun ƙwayoyin, sannan a gurfanar da su a gaban kotu.
