Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 28 ga Satumba, 2026, domin cigaba da sauraron karar da tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya shigar yana neman a hana Shugaba Bola Ahmed Tinubu sake tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027.
Atiku ya shigar da karar ne bisa zargin cewa Shugaba Tinubu ya gabatar wa Hukumar Zabe ta Najeriya, INEC, da takardar shaidar kammala aikin bautar kasa ta NYSC da ake zargin ta bogi ce, tare da bayar da bayanan da ba daidai ba game da sunansa.
Jam’iyyar African Democratic Congress, ADC, ita ce mai kara ta biyu a karar, yayin da Shugaba Tinubu, jam’iyyar APC da INEC suke matsayin wadanda ake kara.
A karar, Atiku ya ce takardar NYSC da aka gabatar wa INEC na dauke da sunan “Tinubu Bola Adekunle”, wanda ya ce ba sunan Shugaban kasar ba ne.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bukaci kotu ta bayyana cewa ko gabatar da wannan takarda ya sabawa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Najeriya da suka shafi cancantar tsayawa takarar shugaban kasa.
Ya kuma nemi kotu ta hana Tinubu da APC shiga zaben shugaban kasa na 2027.
A zaman kotun na ranar Talata, lauyoyin da ke wakiltar Shugaba Tinubu sun bayyana a gaban kotun.
Sai dai lauyan Atiku, Joseph Onu, ya shaida wa kotun cewa har yanzu ba a samu damar mikawa Shugaban kasa kwafin karar da kansa ba.
Ya ce saboda muhimmancin shari’ar, Atiku na son ya mikawa Tinubu takardun da kansa, ko kuma kotu ta ba da umarnin a isar da su ta wata hanya dabam.
“Mai shari’a, wannan muhimmiyar kara ce, kuma ba ma son a bar wata dama da za a yi amfani da wata dabara ta shari’a,” in ji Onu.
Ya kara da cewa wadanda suka shigar da karar za su amince a mika takardun ta hannun lauyoyin Tinubu, idan Shugaban kasar ya bayar da rubutaccen izini da ke ba su damar karbar takardun a madadinsa.
Sai dai lauyan INEC, Dr Alex Iziyon, SAN, ya yi adawa da bukatar a mikawa Tinubu takardun da kansa.
Ya ce kasancewar lauyoyin Shugaban kasar a kotun ya isa a dauki matakin cewa an sanar da bangaren Shugaban kasar game da karar.
INEC ta kuma bukaci kotun ta gaggauta sauraron karar, tana mai cewa sama da kwanaki 17 kenan tun lokacin da aka shigar da ita.
Hukumar ta ce a shirye take ta gabatar da martaninta cikin kwanaki 10.
Bayan sauraron bangarorin, Mai Shari’a Inyang Ekwo ya ce ba zai iya tsara wa masu kara yadda za su tafiyar da shari’arsu ba, sannan ya dage karar zuwa ranar 28 ga Satumba domin cigaba da shari’ar.
Alkalin ya kuma gargadi dukkan bangarorin da lauyoyinsu da kada su rika tattauna bayanan shari’ar da ke gaban kotu a kafafen yada labarai ko shafukan sada zumunta.
“Ya kamata a gudanar da wannan shari’a a kotu, ba a kafafen yada labarai ba.” in ji Mai Shari’a Ekwo.
