Rundunar Sojin Sama ta Kasa ta tura tawagar bincike zuwa kasuwar mako-mako ta Jilli da ke kan iyakar jihohin Borno da Yobe, bayan rahoton aukuwar harin bam da ya shafi fararen hula.
Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Aneke, ya bayar da umarnin a gudanar da bincike nan take kan lamarin, inda ya ce rundunar tana ɗaukar duk wani rahoton da ya shafi fararen hula da muhimmanci da tausayi.
Mai magana da yawun rundunar, Iya Komodo Ehimen Ejodame, ya bayyana hakan cikin sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi, inda ya ce rundunar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen gano hakikanin lamarin.
Rahotanni sun nuna cewa aƙalla mutane 56, mafi yawansu ’yan kasuwa, ake zargin sun rasa rayukansu, yayin da wasu 14 ke jinya a asibiti sakamakon harin da ya auka a kasuwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa an kafa kwamitin bincike na musamman domin gudanar da bincike a wurin da lamarin ya faru.
Rundunar Sojin ta jaddada cewa za ta ci gaba da kare tsaron ƙasa tare da kiyaye rayukan al’umma, tana mai kira ga jama’a da kafafen yaɗa labarai da su guji yada jita-jita har sai an kammala bincike.
