An shiga fargaba a jihar Oyo bayan da wasu ƴan ta’adda ɗauke da makamai suka kai hari a lokaci guda kan makarantu uku da ke ƙaramar hukumar Orire, tare da kashe mataimakin shugaban makaranta guda, kuma suka yi garkuwa da ɗalibai da malamai da dama, lamarin da ya jefa al’ummomin yankin cikin ruɗani.
Makarantun da lamarin ya shafa sun haɗa da makarantar Baptist Nursery and Primary School da ke Yawota, Community Grammar School da ke Esiele, da kuma L.A. Primary School.
Jaridar punch ta rawaito cewa mazauna yankin sun bayyana harin a matsayin ɗaya daga cikin mafi muni da aka kaiwa makarantu a baya-bayan nan, inda aka ce maharan sun gudanar da harin da rana tsaka tare da zirga-zirga tsakanin wurare ba tare da wani tsoro ba.
Lamarin da ya faru a safiyar ranar Juma’a ya jefa iyaye, malamai da mazauna yankin cikin damuwa, yayin da jami’an tsaro suka fara farautar waɗanda suka yi garkuwa da mutanen.
