Ƙungiyar Likitoci Mata ta Najeriya, reshen jihar Kano, ta shirya dasa bishiyoyi 400 a faɗin jihar, a wani ɓangare na bikin cika shekaru 50 da kafuwar ƙungiyar.
Shirin, wanda aka fara ranar Talata, 24 ga Nuwamba, 2026, ana sa ran kammala shi ranar Asabar, 28 ga watan, inda ƙungiyar ke ziyartar makarantu domin dasa bishiyoyi tare da wayar da ɗalibai kan muhimmancin kiyaye muhalli.
Ƙungiyar ta bayyana cewa dasa bishiyoyi na da muhimmanci wajen rage zafin yanayi, inganta ingancin iska, samar da inuwa da kuma kare muhalli daga gurɓatawa.
Da take jawabi a yayin shirin, shugabar ƙungiyar, Prof. Hadiza Shehu Galadanchi, ta bayyana muhimmancin dasa bishiyoyi wajen inganta muhalli da kuma kare lafiyar al’umma.
Haka kuma, shugabar Medical Women’s Association of Nigeria (MWAN), Dr. Safiya Gambo, ta jaddada muhimmancin ci gaba da gudanar da ayyukan da za su amfani al’umma, musamman waɗanda suka shafi inganta lafiya da kare muhalli.
A nata jawabin, Principal ɗin makarantar GGASS Tudun Murtala, Hajiya Sadiya Muhammad, ta gode wa ƙungiyar bisa zaɓar makarantar domin gudanar da shirin, tana mai cewa dasa bishiyoyin zai taimaka wajen inganta muhalli da kuma wayar da kan ɗalibai game da muhimmancin kiyaye bishiyoyi.
Shirin dashen bishiyoyi 400 na daga cikin ayyukan da ƙungiyar ta tsara domin murnar cika shekaru 50 da kafuwarta, tare da ƙarfafa gudummawarta wajen inganta lafiya da muhalli a Kano.
