Matatar Dangote ta dawo da sayar da man fetur da Naira bayan dakatar da sayarwar na tsawon mako guda.
Sai dai sauyin ya zo ne tare da ƙarin farashin fetur da Naira 140 a kowace lita, inda sabon farashin ya kai N1,215 kan kowace lita.
A baya, matatar ta koma karɓar dalar Amurka wajen sayar da fetur sakamakon ƙarancin ɗanyen mai da take samu daga cikin gida, ƙarƙashin yarjejeniyar musayar ɗanyen mai da Naira.
Ƙungiyar Dillalan Man ta IPMAN ta bayyana cewa matakin zai taimaka wajen inganta wadatar man fetur a faɗin ƙasar.
