Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya taya Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi na II, murnar cika shekaru 65 da haihuwa, inda ya bayyana shi a matsayin shugaba mai hangen nesa da ke bawa jama’a kwarin gwiwa ta hanyar hikima da jajircewa wajen tabbatar da adalci.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, inda gwamnan ya yabawa Sarkin bisa gudunmawar da ya bayar wajen gina ƙasa, bunƙasa ilimi, ci gaban tattalin arziki.
Gwamnan ya ce Mai Martaba Sarkin ya shahara wajen inganta zaman lafiya, haɗin kai da shugabanci nagari, tare da fafutukar tallafawa ilimi, ƙarfafa mata da matasa, da kuma bunƙasa ci gaba mai ɗorewa da sauye-sauyen tattalin arziki.
Gwamna Abba ya kuma addu’ar tsawon rai da hikimar ci gaba da jagorantar Masarautar Kano tare da ba da gudunmawa wajen ci gaban jihar da ƙasa baki ɗaya, tare da jaddada aniyar gwamnatinsa ta ci gaba da aiki kafaɗa da kafaɗa da masarautun gargajiya domin inganta rayuwar jama’a da ci gaban Kano.
