Saurari premier Radio
27.4 C
Kano
Saturday, September 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiHukumar zabe ta jihar Kano ta rage lokacin gudanar da zaben kananan...

Hukumar zabe ta jihar Kano ta rage lokacin gudanar da zaben kananan hukumomi

Date:

Hukumar zabe mai zaman ta jihar Kano KANSIEC ta rage lokacin gudanar da zaban kananan hukumomi zuwa ranar 26 ga watan Oktoban 2024, sabanin ranar 30 ga watan Nuwamba da ta sanya a baya.

Shugaban hukumar, Ferfasa Sani Lawan Malunfashi ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudunar yau Juma’a.

Ya ce sun rage lokacin gudanar da zaban ne domin biyayya ga hukuncin da kotun koli ta yi na bai wa kananan hukumomi yancin cin gashin kansu.

Ferfasa Lawan Malunfashi ya kara da cewa, dukkanin harkoki siyasa za a fara gabatar da su ne daga ranar 1 ga watan Satumba mai kama wa zuwa daren 25 ga watan Oktoba.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...