Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ta wallafa sunan Oladipupo Adebutu a matsayin ɗan takarar gwamnan Jihar Ogun na jam’iyyar PDP a zaɓen 2027.
Mai shari’a Peter Lifu ya bayar da umarnin a ranar Juma’a, 13 ga Nuwamba, 2026, inda ya bai wa hukumar wa’adin sa’o’i 24 ta aiwatar da hukuncin.
Alkalin ya bayyana cewa INEC ba ta da ikon cire sunan ɗan takarar da jam’iyya ta tsayar bisa ƙa’ida ba tare da hukuncin kotu ba.
Ya kuma ce cire sunan Adebutu ya saɓa wa kundin tsarin mulki da haƙƙinsa na samun adalci.
Tun da farko, PDP da Adebutu sun shigar da ƙara a ranar 22 ga Oktoba, bayan da INEC ta cire sunansa daga jerin ’yan takarar gwamnan Ogun da aka wallafa ranar 10 ga Oktoba.
