Majalisar Wakilai ta dakatar da zamanta na tsawon mako guda, sakamakon zanga-zangar da wasu ’yan kwangila suka gudanar a ƙofar shiga ginin majalisa ta ƙasa da ke Abuja,
Masu zanga-zangar sun yi haka ne saboda rashin biyan kuɗaɗen ayyukan da suka kammala tun shekarar 2024.
Rahotanni sun ce ’yan kwangilar sun yi dandazo ne a ƙofar shiga majalisar a ranar Talata, domin nuna rashin jin daɗinsu kan yadda gwamnati ta gaza biyansu haƙƙoƙinsu duk da cewa sun kammala ayyukan da aka ba su.
- Kungiyoyin SSANU da NASU Za Su Yi Zanga-zangar kasar baki daya
- Jami’an Tsaro Sun Tarwatsa Zanga-Zangar Nnamdi Kanu a Abuja
- Matasa sun gudanar da zanga-zanga kan ƙaruwar talauci
Bayanai sun ce masu zanga-zangar sun rufe hanyoyin shiga da fita na majalisar, abin da ya tilasta shugaban majalisar da sauran ’yan majalisa jinkirta zaman da aka shirya gudanarwa.
Wasu daga cikin ’yan kwangilar sun shaida wa manema labarai cewa sun gaji da alkawuran da gwamnati ke ci gaba da yi ba tare da cika su ba, inda suka yi kira da a gaggauta biyansu haƙƙoƙinsu kafin su sake komawa bakin aiki.
Majalisar ƙarƙashin jagorancin mataimakin kakakinta, Benjamin Okezie Kalu ta ce, an dakatar da zaman ne domin ba wa hukumomin da abin ya shafa damar tattaunawa da ’yan kwangilar, da nufin warware matsalar cikin lumana.
