Gwamnatin Kano ta ce zata yi amfani dukkan karfin da doka ta amince mata wajen yin yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da masu safarar su zuwa jihar domin kawo karshen matsalolin da suke haifarwa ga al’ummar Kano.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan lokacin hukumar hana sha da fataucin miyagun Kwayoyi ta kasa reshen Kano NDLEA take bikin kona miyagun kwayoyi masu yawan Tan 12.2 a jihar.
Gwamna Abba wanda Sakataren gwamnatin Jihar Alhaji Umar Ibrahim Farouk ya wakilta ya ce gwamnati ta tura jami’an tsaro sama da dubu guda zuwa wurare 52 da ake zargin aikata laifuffuka a fadin jihar, lamarin da ya kai ga kama masu fataucin miyagun kwayoyi da kuma kwace tarin haramtattun kwayoyi.
Gwamna Yusuf ya ce gwamnatin sa ta ƙaddamar da shirin Tudun mun tsira wato Safe Corridor Initiative domin bada shawara, gyaran hali da sake dawo da masu shaye-shaye cikin al’umma, tare da baiwa NDLEA motocin aiki guda uku domin ƙarfafa ayyukanta.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Shugaban NDLEA na ƙasa, Birgediya Janar Mohammed Buba Marwa mai ritaya,wanda Ahmed Sule Ningi ya wakilta ya ce lalata miyagun kwayoyin alama ce ta kare rayuka da al’umma daga illolin shaye-shaye, yana mai gargadin masu safarar kwayoyin cewa Najeriya ba za ta miƙa wuya ga masu aikata irin laifukan ba.
