Saka ya taimaka wajen ɗaukar nauyin tiyata 120 ga yara a Kano, Najeriya, ta hannun ƙungiyar agaji ta BigShoe.
Bukayo Saka ya samu lambar yabo ta Sócrates saboda tallafin jin ƙai
Ɗan wasan Arsenal da tawagar Ingila, Bukayo Saka, ya samu lambar yabo ta Sócrates a bikin Ballon d’Or, wadda ake bayarwa ga ’yan wasan ƙwallon ƙafa da ke amfani da tasirinsu wajen tallafa wa al’umma.
Haka kuma, ya tallafa wa ayyukan jin ƙai ga iyalan da girgizar ƙasa ta shafa a Turkiyya, tare da bayar da gudummawar kayan makaranta sama da guda 1,000 ga yara a yankin da ya taso a Ingila.
Wannan lambar yabo na nuna cewa tasirin ɗan wasa bai tsaya ga nasarorin da yake samu a filin wasa kawai ba, har da irin gudummawar da yake bayarwa wajen inganta rayuwar al’umma.
Bukayo Saka Tauraro a filin wasa, abin koyi a cikin al’umma.
