Aminu Abdullahi Ibrahim
Hukumar kula da makarantu masu zaman kansu ta jihar ta ce zata samar da kotun tafi da gidanka wacce zata rinka hukunta makarantun dake karya dokokin gwamnati.
Shugaban hukumar kwamaret Baba Abubakar Umar ne ya bayyana haka yayin tattaunawarsa da Premier Radio.
Ya ce hukumar ba zata lamunci mutanen dake bude makarantu gaba gadi ba tare da yin rijista da gwamnati ba.
Kwamaret Baba Umar ya kara da cewa gyaran dokar hukumar da majalisar dokokin Kano ta yi ya rage harajin da take karba daga kaso 15 zuwa kaso 7.5 a hannun makarantun kudi, a don haka ba zata kyale makarantun su rinka tsauwalawa iyayen yara ba.
Kwamaret Baba Abubakar Umar, ya kuma jaddada cewa haramun ne tilastawa iyayen yara sayen litattafai ko wasu kayayyaki.
