Saurari premier Radio
25.8 C
Kano
Saturday, September 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiShugaba Bola Tinubu ya amince da sake gina babbar gadar Wagga da...

Shugaba Bola Tinubu ya amince da sake gina babbar gadar Wagga da ta haɗa jihohin Adamawa da Borno.

Date:

Shugaba Bola Tinubu ya amince da sake gina babbar gadar Wagga da ta haɗa jihohin Adamawa da Borno, bayan rushewar ta karo na biyu cikin watanni biyu.

Mohammed Goni, Darakta Janar na hukumar cigaban Arewa Maso Gabas ne ya sanar da wannan yayin duba wurin da lamarin ya faru a ranar Lahadi a ƙaramar hukumar Madagali ta jihar Adamawa.

Gadar, wadda take da matuƙar muhimmanci wajen sauƙaƙe tafiye-tafiye tsakanin jihohin biyun, ta lalace ne sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya.

Goni ya bayyana cewa bayan binciken farko, an shirya fara gyaran gadar, amma rushewar da ta sake yi ne ya sa aka yanke shawarar sake gina ta gaba ɗaya.

Ya shaida cewa daminar bana na iya jinkirta fara aikin, amma za a ɗauki matakan wucin gadi don ba da damar zirga-zirgar motoci.

Ya tabbatar wa mazauna yankin cewa amincewar da Shugaba Tinubu ya yi za ta kawo sauƙi kuma ta rage wahalhalun da mutane ke fuskanta yayin tafiya tsakanin Adamawa da Borno.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...