An shiga ruɗani a ranar Talata a babbar ƙofar harabar Majalisar Dokoki ta Ƙasa, bayan jami’an Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye kan masu zanga-zanga da suka taru domin nuna rashin amincewarsu da wasu tanade-tanaden gyaran Dokar Zaɓe.
Rikicin ya ɓarke ne lokacin da wasu daga cikin masu zanga-zangar suka yi yunƙurin shiga cikin harabar ginin Majalisar da ƙarfi, suna adawa da matakin Majalisar Dattawa na amincewa da amfani da tsarin aika sakamakon zaɓe ta na’ura tare da tattara sakamako a rubuce a inda fasahar zamani ta gaza. A sakamakon haka, jami’an tsaro suka harba hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa taron.
Hakan ya haddasa tarzoma, inda daruruwan masu zanga-zangar, musamman mata, suka rika guje-guje cikin firgici, wasu ma suna faɗawa kan juna yayin da suke neman mafaka.
Rahotanni sun nuna cewa wata mata mai matsakaicin shekaru ta suma bayan ta shaki hayakin da aka watsa.
- Gwamnatin Kano ta ba da umarnin bibiyar batun yaran jihar da aka kama a zanga zanga
- Rikici ya barke a zauren majalisar wakilai kan yunkurin soke gyaran dokar zaɓe
- Za Mu Kawar Da APC A Mulki A Zaben 2027 – Atiku Abubakar
A yayin zanga-zangar, tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya bayyana cewa babu ja da baya kan buƙatar a rika aika sakamakon zaɓe ta na’ura kai tsaye ba tare da tangarda ba. Ya ce za su ci gaba da matsin lamba har sai an tabbatar da aika sakamako kai tsaye a ainihin lokacin da ake ƙidaya kuri’u.
Dalung ya jaddada cewa fafutukar ba ta samo asali daga son kai ko adawa ta siyasa ba, sai dai domin tabbatar da sahihancin zaɓe da kare mutuncin tsarin dimokuraɗiyya a ƙasar nan.
Haka zalika, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa kuma mai fafutuka, Omoyele Sowore, ya yi kira ga ‘yan Najeriya, musamman matasa, da su ƙara jajircewa wajen neman gyara a tsarin zaɓe. Ya ce dole ne a faɗaɗa fafutukar ta hanyar haɗa kai da kuma shiga harkokin siyasa domin tabbatar da sauyi mai ɗorewa.
Ko da yake adadin masu zanga-zangar bai kai mutum 500 ba, masu shirya taron sun nuna kwarin gwiwa cewa idan aka samu gagarumar fitowar jama’a, hakan zai ƙara matsa wa shugabanni lamba su saurari buƙatun al’umma.
