Ministan harkokin cikin gida Dakta Olubunmi Tunji-Ojo ya bayyana cewa, ‘yan kasashen waje 170 ne suka mika takardar neman zama ‘yan Najeriya.
Ministan ya bayyan hakan ne a jawabinsa a wani taro na kwamitin ba da shawara kan batun zama ‘yan Najeriya a Abuja
Dakta Tunji – Ojo ya jaddada cewa akwai matakai daban-daban da aka tanada ga masu son zama ‘yan Najeriya.
Domin tabbatar da nagartarsu, kuma za su yi la’akari da baki dayansu wajen tantance masu bukatar neman zama ‘yan Najeriya.
Mambobin kwamitin ba da shawara kan zama ‘yan Najeriya sun hada da babban sakataren ma’aikatar harkokin cikin gida da wakilai daga ma’aikatun harkokin waje da shari’a da jami’an hukumar tsaron (DSS) da Hukumar Shige Da Fice Ta Kasa (NIS).
Ministan ya kuma gargadi ‘yan kasashen ketaren dake kokarin neman damar zama ‘yan Najeriya ta barauniyar hanya da su tuba, domin kuwa ma’aikatar da sauran hukumomin tsaro ba za su daga kafa ba kan duk wanda suka samu da aikata wannan laifi ba.
