Saurari premier Radio
24 C
Kano
Saturday, September 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiYadda zanga-zangar tsadar rayuwa ta janyowa shugabannin hukumomin DSS da NIA rasa...

Yadda zanga-zangar tsadar rayuwa ta janyowa shugabannin hukumomin DSS da NIA rasa mukamansu

Date:

Bayanai na ci gaba da fitowa fili kan dalilan da suka sanya shugaban hukumar tsaro ta DSS, Yusif Bichi da kuma na hukumar leken asiri ta kasa NIA Ahmed Abubakar suka rasa mukamansu.

Jaridar Punch ta rawaito cewa murabus din shugabannin na da alaka da zanga-zangar tsadar rayuwa da kuma yadda wani kamfanin kasar China ya kwace jiragen shugaban kasa.

Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa, shugaban kasa da mai bashi shawara kan tsaro Malam Nuhu Ribado, ba su ji dadin yadda hukumar DSS ta kasa samun bayanan sirri kan irin munin da zanga-zangar tsadar rayuwar za ta yi a wasu jihohin arewacin kasar nan ba gabanin fara yin ta.

Sai kuma sakacin hukumar leken asiri ta kasa NIA, da ta gaza gano shirin kamfanin Zhongshan dake kasar China na kwace jiragen shugaban kasa a Faransa.

Tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari ce dai ta nada shugabannin a shekarar 2018, sai dai wata majiya ta tabbatarwa da jaridar cewa, dama ana takun saka tsakanin tsohon shugaban hukumar tsaro ta DSS, Yusif Bichi da kuma mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro Malam Nuhu Ribado.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...