Saurari premier Radio
25.8 C
Kano
Sunday, September 22, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKotu ta aika da masu zanga-zangar tsadar rayuwa gidan yari

Kotu ta aika da masu zanga-zangar tsadar rayuwa gidan yari

Date:

Babbar kotun tarayya ta Abuja ta aika da mutum 10 da ake zargi da hannu a zanga-zangar tsadar rayuwa zuwa gidan yari.

Mai shari’a Emeka Nwite, ya aika da maza tara gidan gyaran hali na Kuje sannan ya aika da mace É—aya zuwa gidan yarin Suleja.

Mutum goman da aka gurfanar a gaban kotun sun haÉ—a da Michael Adaramoye da Adeyemi Abayomi da Suleiman Yakubu da Opaoluwa Simon da Angel Innocent.

Sauran sun haÉ—a da Buhari Lawal da Mosiu Sadiq da Bashir Bello da Nuradeen Khamis da kuma Abdulsalam Zubairu.

An gabatar da su ne a gaban kotun inda ake tuhumar su da cin amanar ƙasa da yi wa gwamnati bore da kuma yunƙurin hargitsa kasar nan.

Alƙalin ya kuma saka ranar 11 ga watan Satumba a matsayin ranar da zai yanke hukunci dangane da buƙatar bayar da belin waɗanda ake zargin.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...