Xi Jinping da Donald Trump Sun Kammala Ganawa a Koriya ta Kudu Kan Rikicin Kasuwanci.
Shugabanin biyu sun kammala ganawa ne a birnin Busan a Koriya ta Kudu, a inda suka tattauna kan batutuwan da ke haddasa rikice-rikicen kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu.
Ganawar ta fara tun da sanyin safiyar Alhamis, ta kuma ɗauki kusan sa’o’i biyu ba su kammala ba.
Tattaunawar ta su ta mayar da hankali ne kan batutuwa masu muhimmanci da suka shafi huldar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu.
Shugaba Trump ya bayyana gamsuwarsa da yadda tattaunawar ke gudana, yana mai cewa yana da ƙwarin gwiwar cewa za su cimma yarjejeniya mai amfani ga ɓangarorin biyu.
Trump ya kuma bayyana cewa sun cimma matsaya kan ɗage takunkuman kasuwanci da Amurka ta kakaba wa China, musamman waɗanda suka shafi fitar da albarkatun ƙasa masu wuya daraja.
Tun a ranar Laraba a kan hanyarsa zuwa Koriya ta Kudu, Trump ya nuna fatan samun kyakkyawar yarjejeniya tsakaninsa da Xi Jinping.
Ya na mai fatan ganawarsu za ta taimaka wajen kwantar da hankalin kasuwannin duniya da ke fuskantar tashin hankali saboda takunkuman da ɓangarorin biyu suka kakaba wa juna.
