Sabbin hotuna masu kayatarwa da ‘yan sama jannati na Artemis II suka ɗauka sun nuna wata da kuma cikin jirgin Orion spacecraft, inda suke ba da haske kan yadda rayuwarsu take a sararin samaniya yayin da suka cimma wani muhimmin tarihi.
Daya daga cikin hotunan ya nuna wani ɓangare na Orientale basin a jikin wata mai duhu, lamarin da NASA ta ce shi ne karo na farko da idanun ɗan’adam suka gani, domin a baya na’urorin robot ne kawai suka taɓa daukar hotunan yankin.
Wannan babban rami mai inuwa, wanda faɗinsa ya kai kilomita 965, yana nuna muhimmin wuri tsakanin gefen wata na kusa da duniya da kuma na nesa.
‘Yar sama jannati Christina Koch ta bayyana ganin gefen wata da ke fuskantar nesa da duniya a matsayin abin ban mamaki matuƙa. Ta ce: “Akwai wani abu da ke sa ka ji cewa wannan ba shi ne irin watan da ka saba gani ba.”
Hotunan da aka ɗauka daga cikin jirgin Orion sun sauya daga mayar da hankali kan kyawun duniya daga nesa zuwa nuna yadda wata ke ƙara bayyana yayin da suke ƙara kusantarsa.
Sun kuma ce watan na ci gaba da bayyana yana ƙara girma a cikin tagogin jirgin Orion yayin da tafiyar ke ci gaba.
Haka kuma, hotunan duniya da aka ɗauka sun kasance masu ban sha’awa, inda suka nuna yadda duniyarmu ke kama daga nesa — wani abu da ba a gani da idanun ɗan adam ba tun zamanin kumbo Apollo.
Baya ga haka, ‘yan sama jannatin na ci gaba da bayyana kai tsaye a cikin shirye-shiryen labarai na NASA, suna ba da damar ganin yadda rayuwarsu ke gudana a sararin samaniya.
