Daga Zainab Muhammad Sani
Dakarun rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) sun daƙile harin da ’yan ta’addan ISWAP suka kai a garin Gamborun Ngala da ke kan iyakar Najeriya da ƙasar Kamaru.
An kai harin ne da misalin ƙarfe 6:15 na yammacin ranar Asabar,
Rahotannin sun ce an ji ƙarar harbe-harbe masu ƙarfi a sassa daban-daban na garin a yayin garin.
Sojojin sun mayar da martani cikin gaggawa, inda suka shiga fafatawa da ’yan ta’addan, kuma suka fatattake su ba tare da wata asara a ɓangaren dakarun ba, a cewar wasu majiyoyi.
Aminiya ta rawaito cewa babu wani soja ko farar hula da ya rasa ransa ko ya jikkata, yayin da aka samu cikakken kwanciyar hankali a garin bayan da aka daƙile harin.
