
Aminu Abdullahi Ibrahim
Tsohon Gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi, ya ce shugabannin addinai suna da cikakken ‘yancin su soki gwamnati idan sun ga akwai buƙatar hakan.
Amaechi ya bayyana haka ne yayin wata hira da ya yi da Channels TV, inda yake martani kan sukar da wasu limaman Cocin Katolika suka yi wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ya ce aikin shugabannin addinai ba wai wa’azi kawai ba ne, suna da alhakin faɗakar da gwamnati da al’umma kan batutuwan da suka shafi adalci, jin daɗin jama’a da shugabanci nagari.
A cewarsa, idan gwamnati ta yi abin da bai dace ba, babu laifi shugabannin addinai su fito su bayyana ra’ayinsu cikin gaskiya da adalci.
Kalaman Amaechi na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara kan sukar da wasu shugabannin addinai ke yi wa manufofi da ayyukan gwamnatin tarayya.
