Gwamnan jihar Kogi Usman Ahmed Ododo ya alakanta matsalolin tsaro da ake samu a yankin Arewa ta tsakiya da kwararowar ‘yan ta’adda daga Arewa maso Gabas, da kuma Arewa maso Yamma.
Gwamna Usman Ododo ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyarar jaddada goyon baya ga shugabancin jam’iyyar APC na kasa, karkashin jagorancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje, a sakatariyar jam’iyar dake Abuja.
Gwamna Ododo ya ce, ya zama wajibi a hada kai tsakanin gwamnati da jami’an tsaro domin magance kwararowar masu aikata laifuka zuwa wasu jihohin.
Ya kara da cewa an samu nasarar kashe da yawa daga cikin wadanda suka kai hare hare a jihar Kogi, yana mai kara jaddada ƙudirin gwamnatinsa na kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.
Jawabin na Gwamna Ododo na zuwa ne kwanaki biyu bayan da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci jihar Benuwe domin jajantawa al’ummar jihar kan kashe-kashen da aka yi a Yelewata a ranar 13 ga watan Yuni.
