Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya ce Allah ne kaɗai yake da ikon bayar da shugabanci ga wanda ya nufa, kuma babu wani mutum ko ƙungiya da yake da ikon bada mulki ko hanawa.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga alhazan Kano da jami’an aikin Hajji a birnin Makkah a lokacin ziyarar Sallah da ya kai musu.
A cewar gwamnan, duk da cewa wasu na ganin za su iya tasiri wajen zaɓen shugabanni, ikon mallakar mulki gaba ɗaya yana hannun Allah ne, wanda shi ne yake bada mulki kuma yake ƙwace shi ga wanda ya so.
Gwamna Abba ya ce shugabanci amana ce daga Allah, kuma tuni ya mika lamarinsa ga Ubangiji dangane da duk wani abu da ya shafi makomar siyasa, yana mai nuna yakinin cewa abinda Allah Ya ƙaddara shi ne zai tabbata, tare da bukatar alhazan da su tabbatar suna da katin zaɓe tare da kira ga waɗanda katunansu ke buƙatar sabuntawa da su gaggauta yin hakan kafin wa’adin rajista da sabuntawa ya ƙare.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf na cewa gwamnatinsa ta samu nasarori masu yawa a cikin shekaru uku da suka gabata, musamman a fannoni irin su ilimi, lafiya, noma, gina ababen more rayuwa, da kuma tallafawa mata da matasa.
