Jagoran jam’iyyar NDC na ƙasa, Sanata Seriake Dickson, ya yi kakkausan gargaɗi ga magoya bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Peter Obi da mataimakinsa Rabi’u Kwankwaso da su daina cin mutuncin jam’iyyar da kuma rage darajarta.
Yayin da yake hira a shirin Prime Time a gidan talabijin na Arise TV, tsohon gwamnan jihar Bayelsa ya ƙaryata jita-jitar da ake yadawa na rikicin cikin gida da jam’iyyar ke fama dashi, yana mai jaddada cewa jam’iyyar ce ke yi wa yan takarar alfarma ta hanyar ba su takara, ba wai akasin haka ba.
A jawabinsa ga magoya bayan yan takarar, Dickson ya jaddada sadaukarwar da shugabannin jam’iyyar suka yi tun kafin manyan yan siyasar su shigo cikinta.
Inda ya ce “Peter Obi mamba ne a jam’iyyar mai girma. Mu da kanmu muka ba shi tikitin takarar shugaban ƙasa shi kaɗai, kuma wannan abu ne mai muhimmanci. Babu ɗayansu da ya kasance cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar lokacin da muka yi mata rajistarta.
Ya kara da cewa ’’Ba su biya ko sisi ba, babu wani ɗan takarar shugaban ƙasa da ya biya ko sisi.”
Dangane da batutuwan zaɓe gaba ɗaya, Sanata Dickson ya soki tsoma bakin majalisar dokoki ta ƙasa da ke yi cikin harkokin gudanar da jam’iyyu, yana mai cewa ba huruminsu ba ne su tilasta tsarin zaɓen fidda gwani kai tsaye ga jam’iyyun siyasa.
