Rukunin farko na yan Najeriya da aka kwaso daga kasar Afrika ta Kudu sakamakon sabbin hare-haren ƙiyayyar baƙi ya isa Lagos.
Jimillar mutane 268 ne suka sauka a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Lagos a ranar Alhamis ta jirgin Air Peace, wanda aka shirya a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin gwamnatin tarayya na dawo da yan Najeriya zuwa gida.
Jirgin wanda da farko aka tsara zai tashi ranar Litinin, an samu jinkiri zuwa Laraba sakamakon matsalolin takardu da gudanarwa.
Dawo da yan ƙasar ya biyo bayan ƙarin hare-hare kan yan Najeriya da ke zaune a Afirka ta Kudu, inda rahotannin hare-haren ƙiyayyar baƙi suka sa yawancin yan ƙasashen waje neman taimako domin komawa ƙasashensu.
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa fiye da yan Najeriya 1,000 sun nuna aniyarsu ta barin Afirka ta Kudu domin dawowa gida, tare da ƙarin jiragen dawo da wasu da ake sa ran za su biyo baya cikin kwanaki masu zuwa.
Ministar harkokin wajen Najeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, ta ce yawan yan Najeriya da ke neman a dawo da su na ci gaba da ƙaruwa.
Ta ce ofishin jakadancin Najeriya da ke Pretoria ya tattauna da hukumomin Afirka ta Kudu domin sauƙaƙa dawowar yan ƙasar, ciki har da waɗanda ke fuskantar matsalolin takardun zama.
Isowar rukunin farko na nuna fara wani babban shiri na taimaka wa yan Najeriya da rikicin ya shafa tare da tabbatar da sun dawo gida cikin koshi lafiya.
