Sarkin na Kano ya ce wadannan yan kasuwa su je Legas ne domin su koya musu yadda ake kasuwanci, ba wai su koyi kasuwanci ba.
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana haka ne yayin da ya ke jawabi a taron ƙungiyar sakatarori da kwararru a aikin gwamnati ta ICSAN.
Sarkin ya ce Kano jiha ce mai tsohon tarihi na kasuwanci, wanda yasa ta samar da waɗannan hazikan yan kasuwa.
Ya kuma ce ko a baya jihar ta saba samar da irin waɗannan ƴan kasuwa waɗanda suka bunƙasa a fannin kasuwanci.
Ana ganin kalaman sarki Sanusi a matsayin martani ga mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima wanda a ranar Litinin ya ce “Lagos ce ta samar wa Afirka attajirinta mafi arziki, ba Kano ba. Aliko Dangote ɗan Lagos ne. Haka kuma, ba Kano ba ce ta ba Afirka attajiri na biyu mafi arziki, Abdul Samad Rabi’u”
Shettima ya yi wannan bayani ne a taron Invest Lagos Summit 3.0 da aka gudanar a ranar Litinin, inda ya yaba wa jihar Lagos, tsarin shugabancinta da kuma rawar da take takawa wajen gina arzikin ƙasa.
