Kamfanin jiragen sama na Air Peace ya cire wani fasinja daga cikin jirginsa da zai tashi zuwa Abuja, bayan wani rikici da ya barke tsakanin fasinjan da ma’aikatan jirgin.
Rahoton da hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasa ta wallafa ya bayyana cewa fasinjan mai suna Celestine Ezeudu ya ƙi bin umarnin ma’aikatan jirgin na dakatar da ɗaukar hotuna da kuma ajiye wayarsa yayin da jirgin ke shirin tashi.
Daraktan hulɗa da jama’a da kare haƙƙin masu amfani da hukumar NCAA, Michael Achimugu, ya ce lamarin ya ƙara tsananta ne lokacin da fasinjan ya yi wata magana da aka fassara da cewa fushinsa na iya ƙona jirgin.
Ya ce bayan samun labarin abin da ya faru, kyaftin ɗin jirgin ya dakatar da shirin tashi tare da mayar da jirgin inda aka cire fasinjan.
Hukumar NCAA ta bayyana cewa an dauki matakin ne domin tabbatar da tsaron fasinjoji da ma’aikatan jirgin, musamman a lokacin da jirgin ke shirin tashi.
