Rundunar yan sanda jihar Gombe ta ce ta yi nasarar lalata sansanin ‘yan bindiga, tare da kama mutum bakwai daga cikinsu da kuma makamansu.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito rundunar yan sandan ta gudunar da wannan aikin ne, hadin gwiwa da ƙungiyar mafarautan jihar wadanda suka yin aiki tare da juna domin tabbatar da zaman lafiya.
Daga cikin wadanda yan sandan suka kama sun hadar da wani mai suna Abdullahi Ibrahim, a ƙauyen Tilde ranar 23 ga watan Nuwambar data gabata, inda ya bayyana sunayen abokan hulɗarsa da suke yin garkuwa da mutane a jahohin Gombe da Bauchi da kuma Adamawa.
- An Takaita Zirga-Zirga Dare a Gombe
- Gwamnatin Gombe ta ceto yara 59 da aka sace a watanni 8
- Ma’aikatan Ƙananan Hukumomin Gombe An Yi Musu Ƙarin Albashin N5,000
Har wa yau rundunar yan sandan ta sake tabbatar da cewa, sun samu nasarar kama mutum shida bayan wata fafatawa da ‘yan bindigar.
Wadanda ake zargin sun amsa laifin abunda ake tuhumar su da aikata wa na satar mutane, da kuma karbar kudin da suka haura sama da nairas miliyan 150.
