Kyaftin din Manchester City Kyle Walker Ya koma kungiyar kwallon kafa ta AC Milan zuwa karshen kakar bana a matsayin aro.
Walker, wanda ya yi wa Man City wasa 316, ya kuma samu nasarar daukar kofuna 15 a tsahon shukarun ya shafe a kungiyar ta kasar Ingila.
Kungiyoyi biyun sun amince da cimma yarjejeniya kan dan wasan, kuma akwai damar siyansa a bazara idan ya kammala zaman aron.
Mai shekara 34 ya yi wa City wasa na karshe a karawarsu da West Ham ranar 4 ga watan Janairun nan, inda a lokacin ya gaya wa Pep Guardiola yana son jarraba sa’arsa a wata kasa.
A shekarar 2017 ne dai dan kasar Ingila Walker, ya koma Manchester daga Tottenham a kan fam miliyan 50..
Sai dai a shekarar 2023 ne ya zama kyaftin City, kuma ya bugawa Ingila wasa 93 jumulla.