
‘Yan bindiga sun kai farmaki garin Garo dake Karamar Hukumar Kabo, Jihar Kano, inda suka sace wata budurwa, bayan duk karɓar Naira miliyan takwas daga danginta.
Majiyoyi sun ce maharan, su goma, sun kutsa gidan wani attajiri, Alhaji Auwal, da misalin ƙarfe 1:20 na dare, inda suka tsoratar da iyalinsa kuma suka tara su a wuri guda.
Duk da an basu kuɗin da suka nema, sun yi awon gaba da ‘yar gidan, wacce ta kammala makarantar sakandare.
Har kawo yanzu ba a ji daga gare su ba, lamarin da ya jefa al’umma cikin fargaba.
Kakakin ‘yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa ana bincike don cafke maharan.