Gwamnan Kano ya nada sabbin shugabannin Kano Pillars
Ahmad Hamisu GwaleÂ
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya nada sabbin shugabanin hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Lahadi, yace Abba Yusuf ya amincewa da nadin sune bayan karewar wa’adin tsaffin Shugabannnin.
A watan da muke ciki ne dai aka sallami Babangida Umar Little daga jagorancin kungiyar da ake yiwa take da sai masu gida.
Ofishin kwamishinan matasa da wasanni, Mustapha Rabiu Kwankwaso ya sanar da cewa an nada mutum 14 da za su ja ragamar Pillars a matakai daban-daban.
Tuni dai aka nada Ali Na Yara mai Samba a sabon shugaban kungiyar a mataki na rikon kwarya na shekara daya tare da karin mutum 12 har da Abubakar Isa Dandago a matakin jami’in yada labaran kungiyar.
Sanarwar ta bayyana sabbin shugabannin za su yi aiki tare da ma’aikatar matasa da wasanni ta jihar da sauran masu ruwa da tsaki domin kai Pillars gaba..
Jerin shugabannin Kano Pillars sun hadar da
Aliyu Nayara Mai Samba – Shugaba
Salisu Muhammad Kosawa – Mamba
Abubakar Isa Dandago – Jami’in yada labarai
Ismail Abba Tangalash- Mataimakin Jami’in yada labarai
Yusuf Danladi Andy Cole – Mamba
Muhammad Usman – Mamba
Ahmad Musbahu – Mamba
Umar Umar Dankura – Mamba
Rabiu Abdullahi – Mamba
Nasiru Bello- Mamba
Muhammad Danjuma Gwarzo – Mamba
Mustapha Usman Darma – Mamba
Muhammad Ibrahim (Hassan West) – mamba
Engr Usman K/Naisa- Mamba.
Haka zalika gwamnan ya nada kaftin É—in Najeriya (Super Eagles) Ahmed Musa, a matsayin jakadan wasanni na jihar Kano.
Tuni dai ake saran fara gasar gasar Firimiyar Najeriya ta kakar wasannin shekarar 2024/2025 daga 31 ga watan Agusta.
Kuma hukumar shirya gasar ta NPFL ta tanadi naira miliyan 200 ga duk kungiyar data lashe gasar Firimiyar Najeriya.